Tambaya ta: 4. Ka ranta Suratul Qari'ah? kuma ka fassarata.

Amsa: Suratul Qari'ah da kuma fassararta:

Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

1. {Mai ƙwanƙwasa 1. 2.Mece ce mai ƙwanƙwasar 2? 3. Kuma wane ne ya sanar da kai abin da ake nufi da Maƙwanƙwashiya 3? 4. Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa 4. 5.Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe 5. 6. To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi 6. 7. Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda 7. 8. Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi) 8. 9. To uwarsa Hawiya ce 9. 10 Kuma me ya sanar da kai mece ce ita 10? 11. Wata wuta ce mai zafi 11}. [Surat Al-Qari'ah: 1 - 11].

FASSARA:

1- {Mai ƙwanƙwasa 1}. Al-ƙiyama tana ƙwanƙwasa akan zukatan mutane saboda girman tashin hankalinta.

2. {Mece ce mai ƙwanƙwasa 2}: Mece ce wannan Al-ƙiyamar wacce take ƙwanƙwasar zukatan mutane saboda girman tashin hankalinta?!.

3. {Kuma me ya sanar da kai mecece mai ƙwanƙwasa 3}: Mene ne ya sanar da kai - ya kai wannan Manzo - mecece wannan Al-ƙiyamar wacce take ƙwanƙwasar zukatan mutane, saboda girman sha'aninta, lalle itace ranar Al-ƙiyama.

4. {Ranar da mutane zasu kasance kamar 'ya'yana fari masu watsuwa 4}: Ranar da zata ƙwanƙwashi zukatan mutane su kasance kamar fari masu yaɗuwa masu tarwatsewa nan da can.

5. {Kuma duwatsu su kasance kamar gashin sufin da aka saɓe}: Duwatsu su kasance kamar gashin sufi wanda aka saɓe, acikin sakin tafiyar su da motsin su.

6. {To, amma wanda ma'aunan sa suka yi nauyi 6}: Amma wanda kyawawan ayyukan sa suka rinjayi munanan ayyukan sa.

7. {To, shi yana cikin wata rayuwa yardadda 7}: Shi yana cikin rayuwa yardadda da zai sameta a cikin Aljanna.

8. {To, amma duk wanda ma'aunansa suka yi sauƙi 8}: Amma wanda munanan ayyukansa suka rinjayi kyawawan ayyukansa.

9. {To, Uwar sa Hawiyace 9}: Masaukin sa da madabbatar sa a ranar Al-ƙiyama ita ce Jahannama.

10. {Kuma me ya sanar da kai menene ita 10}: Me ya sanar da kai - ya kai wannan Manzo - mecece ita?!

11. {Wata wuta ce mai zafi}: Ita wuta ce mai tsananin zafi.